Adamawa: An sace wani Malamin Jami’a bayan an harbe Kaninsa

Adamawa: An sace wani Malamin Jami’a bayan an harbe Kaninsa

Mun ji labari cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san wanene su ba sun yi awon gaba da Malamin jami’ar kimiyyar nan ta tarayya da ke Garin Yola a jihar Adamawa watau Moddibo Adama.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, an sace wannan Malami Farfesa Adamu Zata ne a gidansa da ke Garin Gierei da ke wajen babban birinin Adamawa na Yola a cikin karshen makon jiya.

Wadannan ‘yan bindiga sun bindige ‘danuwan Shehin mai suna Sheda Zara kafin su auko su tafi da shi da karfi da yaji. Zara Likitan dabbobi ne da tsautsayi ya rutsa da shi a cikin dare.

Dr. Zara ya yi yunkurin ya leka domin duba abin da ke faruwa bayan ya ji motsi a cikin gidan. A nan ne ya gamu da ajalinsa bayan da aka sakan masa harsashi a gidan ‘danuwan na sa.

KU KARANTA: Jami'in tsaron da aka yi garkuwa da shi ya samu 'yanci

Wannan ne karo na biyu da aka yi garkuwa da Malamin jami’ar a gidansa. Shekara guda da ya wuce, wasu ‘yan bindiga sun sace shi a Watan Oktoba har sai da aka biya su Miliyan biyu.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan labari inda ya bayyana cewa jami’an ‘yan sandan kasar sun soma bincike.

Sulaiman Nguroje ya bada karin bayani da cewa wadannan Miyagu sun aukawa gidan ne da kimanin karfe 2:00 na dare. Gawar Sheda Zara ta na ajiye a babban asibitin da ke Garin Yola.

Sheda Zara wanda ya riga mu gidan gaskiya ya rasu ne ya na da shekara 49 daga kai wa ‘Danuwan na sa ziyara. Kawo yanzu babu labarin inda aka kai Malamin na jami’ar ta MAUTECH.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel