Majalisar wakilai za ta rantsar da kwamitocinta a ranar Laraba

Majalisar wakilai za ta rantsar da kwamitocinta a ranar Laraba

Majalisar wakilai za ta rantsar da kwamitoci sama da guda 100 a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba. Shugaban kwamitin majalisa kan harkokin labarai da jama’a, Benjamin Kalu ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ne ya kafa tare da sanar da kwamitocin a zauren majalisa a farkon watan Yuli.

Daga bisani sai majalisar ta tafi hutu sannan ta dawo a farkon watan Satumba sannan tun daga lokacin tana ya tattauana lamura daban-daban da kuma dokoki.

Ta kuma gabatar da wasu kuduri tare da sauran ayyukan majalisa.

Rantsar da kwamitocin na musamman zai ba majalisar damar gudanar da ayyukanta na ma’aikatu, hukumomi da sauransu.

KU KARANTA KUMA: MURIC tace Najeriya bata taba samun shugaba tamkar Buhari ba tun bayan samun yancin kai

A wani lamarin kuma mun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Najeriya tana asarar dukiya ta kimanin naira tiriliyan biyar a duk shekara sanadiyar satar danyen mai daga bututan da ke fadin kasar nan.

Wannan rahoto na kunshe cikin wata sanarwa da dan majalisar tarayya mai wakilcin mazabar Aguata ta jihar Anambra, Honarabul Chukwuma Umeoji, ya gabatar a ranar Alhamis kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel