Romon Dimokradiyya: Dan majalisar APC a jihar Adamawa ya raba wa matasa kyautar baro

Romon Dimokradiyya: Dan majalisar APC a jihar Adamawa ya raba wa matasa kyautar baro

Maigari Bello Kasimu, mamba mai wakiltar Jalingo, Yorro da Zing a majalisar wakilai, ya raba kyautar baro ga mambobin kungiyar masu tura baro a mazabarsa da ke jihar Adamawa, a matsayin daya daga cikin aiyukan da 'yan majalisu ke yi ga jama'ar mazabunsu.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Saidu Giwa Na-annabi, hadimin dan majalisar, shine ya wakilci dan majalisar yayin rabon baron ga mambobin kungiyar masu tura baron.

Da yake magana da manema labarai, wakilin dan majalisar ya koka a kan rashin aiki a tsakanin matasa tare da bayyana cewa rashin aiki matsala ce da ta zama ruwan dare a duniya.

"Dukkan wadannan matasa na karbo hayar baro ne domin su yi sana'ar da zasu samu abinci, amma yanzu sun samu damar mallakar baro tasu ta kansu," a cewarsa.

Dan majalisar ya bukaci matasan da suka samu kyautar baron da su ga hakan a matsayin kalubale da kuma wata dama ta bunkasa rayuwarsu daga kudin da suke samu daga sana'arsu.

Ya yi kira ga matasan da su yi amfani da karfinsu wajen gyara rayuwarsu a yanzu domin gobensu, a lokacin da karfinsu ya ragu.

Kazalika, dan majalisar ya gargadi matasan a kan tu'ammali da miyagun kwayoyi da kuma aikata laifuka.

A nasa bangaren, Aliyu Jidda, daya daga cikin wadanda suka samu, ya bayyana jin dadinsa tare daukan alkawarin yin amfani da damar wajen inganta tattalin arzikin kansu.

Taron rabon ya samu halartar wasu mambobin jam'iyyar APC da shugabannin kungiyoyin masu tura baro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel