Dukkanin jam’iyyun siyasar Najeriya zamu ne ta tadda muje - Shekarau

Dukkanin jam’iyyun siyasar Najeriya zamu ne ta tadda muje - Shekarau

Sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana dukkanin jam’iyyun siyasa a matsayin miyagu domin dukkaninsu na da kundin tsari da manufa iri guda.

Sanata Shekarau ya bayyana hakan a lokacin lakcan bikin cikar Najeriya shekaru 59 da samun yancin kai wanda cibiyar Hudaibiyya ta shirya, sannan aka gudanar a magarantar kwaleji na Aminu Kano da ke Kano.

A cewarsa, banbancin ya ta’allaka ne akan wanda kake tarayya dashi da kuka kan abunda ya sa kake tarayya dashi domin dukkanin jam’iyyun siyasa na fadin abu iri guda ne.

Ya kara da cewa da ace yan Najeriya na da zabi na samar da nagartaccen shugaba mai kula, da yan Najeriya basu riki damokradiyya a matsayin mafita ba.

KU KARANTA KUMA: MURIC tace Najeriya bata taba samun shugaba tamkar Buhari ba tun bayan samun yancin kai

Sanata Shekarau ya cigaba da shawartan dukkanin yan Najeriya masu din cigaban kasar da su tabbatar da dorewar fafutukar da aka yi wajen cimma matsayin.

A wani laari na daban, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yan Najeriya tabbacin samun wutar lantarki mai dorewa kuma cikin sauki nan ba da jimawa ba.

Da yake magana a ranar bikin yanci na 59 a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, Shugaban kasar yace gwamnatinsa ta yanke shawarar kawo sauyi a ma’aikatar wutar lantarki.

Yayinda tallafin kudin lantarki a gwamnatin Buhari ya doshi naira triliyan 1.5 cikin shekaru biyar, wutar lantarki da ake ba gidajen yan Najeriya ya kasance kasa da megawatts 5,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel