Kotu ta bayar da belin mahaifin da ke haikewa ‘yarsa

Kotu ta bayar da belin mahaifin da ke haikewa ‘yarsa

Wata kotu dake Ikeja a jihar Lagas ta tsare wani mutum mai suna Chinedu Ifeteka, dan shekara 46 da ta samu da laifin yi wa ‘yar cikinsa mai shekaru 14 fyade.

Ifeteka wanda ke sana’ar siyar da kaya a kasuwar Ojo ya karyata aikata laifin da ake tuhumarsa akai.

Alkalin kotun B.O. Osunsanmi ta baya da belin Ifeteka akan N300,000 tare da gabatar da wadanda za su tsaya masa mutum biyu wadanda ke biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas.

Lauyan da ya shigar da karan, Ezekiel Ayorinde ya bayyana cewa Ifeteka ya fara yin lalata da ‘yar tasa tun a ranar 9 ga watan Agusta a gidan su dake Ojo.

Ya ce Ifeteka kan danne ‘yar sa mai shekaru 14 a duk lokacin da matarsa bata a gida.

“Da yarinyar ta gaji da abin da mahaifinta yake yi mata sai ta fadi wa mahaifiyarta inda daga nan ne jami’an tsaro suka samu labari."

KU KARANTA KUMA: Matsalar Najeriya bai da magani ta bangaren siyasa - Kungiyar CAN

Ayorinde yace bisa ga doka hukuncin duk wanda aka kama da laifin aikata haka shine daurin rai da rai a kurkuku.

Za a ci gaba da sauraron shari’ar a ranar 25 ga watan Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel