Yanzu-yanzu: An sako shugabannin NSCDC da aka yi garkuwa da su

Yanzu-yanzu: An sako shugabannin NSCDC da aka yi garkuwa da su

Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Edo ta ce an sako manyan jami'an ta biyu da masu garkuwa da mutane suka sace ranar 27 ga watan Satumban 2019.

Kwamandan rundunar, Mista Makinde Ayinla ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a Benin a ranar Talata.

Ayinla ya ce wadanda su kayi garkuwa da jami'an sun sako su a garin Ebelle da ke karamar hukumar Igueben.

DUBA WANNAN: Kogi: Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana dan takarar da za ta jefa wa kuri'a

Sai dai ya ce ba a biya kudin fansa ba kafin a sako su.

Kwamandan ya mika godiyarsa ga rundunar 'yan sanda da kungiyar 'yan banga na garin Ebelle da iyalan wadanda akayi garkuwa da su.

Ayinla ya kuma yabawa sauran hukumomin tsaro bisa gudunmawa da suka bayar da hadin gwiwa da su kayi don ganin an sako mutanen biyu.

An dai sace jami'an biyu ne misalin karfe biyu na rana tsakanin garin Ebelle da Ewosa a babban ririn Ebelle-Agbor a hanyarsu ta komawa Benin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel