Gwamnoni 3 da ministoci 7 da za su raka Buhari kasar Afrika ta Kudu

Gwamnoni 3 da ministoci 7 da za su raka Buhari kasar Afrika ta Kudu

A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyarar kwanaki uku zuwa kasar Afrika ta Kudu domin tattauna wa a kan walwalar 'yan Najeriya mazauna kasar.

Shugaba Buhari zai kai ziyarar ne bisa bukatar shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, domin tattauna wa a kan hare-haren da aka dinga kai wa bakin haure, musamman Najeriya, a kasar.

Gwamnoni uku da ministoci bakwai da wasu hadimai uku ne zasu raka shugaban Buhari zuwa kasar Afrika ta Kudu.

Buhari zai samu rakiyar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da takwaransa na jihar Ebonyi, Dave Umahi, da gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.

DUBA WANNAN: Singham, tsohon kwamishinan 'yan sanda a Kano ya samu mukami a gwamnatin APC

Ministoci bakwai da zasu raka Buhari sune; Geoffrey Onyeama (ministan harkokin kasashen waje), Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (ministan tsaro), Rauf Aregbesola (ministan harkokin cikin gida), Olamilekan Adegbite (ministan tama da karafa), Maigari Dingyadi (ministan harkokin 'yan sanda), Ambasada Mariam Katagum (karamar ministar saka hannun jari da masana'antu) da Saleh Mamman (ministan lantarki).

A cewar jawabin Garba Shehu, "shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai bar Abuja ranar Laraba domin kai wata ziyarar aiki ta kwana uku zuwa kasar Afrika ta kudu bisa gayyatar shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, domin tattauna walwalar 'yan Najeriya mazauna kasar da kuma kulla sabuwar alaka a tsakanin kasashen biyu.

"A yayin ziyarar, shugaba Buhari zai gana da 'yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta Kudu, domin tattauna wa da su a kan halin da suke ciki tare da basu tabbacin cewa gwamnatin Najeriya za ta cigaba da aiki gwamnatin kasar Afrika domin tabbatar da kare lafiyarsu da dukiyoyinsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel