MURIC tace Najeriya bata taba samun shugaba tamkar Buhari ba tun bayan samun yancin kai

MURIC tace Najeriya bata taba samun shugaba tamkar Buhari ba tun bayan samun yancin kai

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) tace gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari tafi dukkanin gwamnatocin da Najeriya tayi tun bayan da ta samu yanci a 1960.

A wani jawabi da ya saki a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, daraktan MURIC, Ishaq Akintola, yace cin hanci da rashawa ya kasance babban matsalar Najeriya sannan kuma gwamnatin Buhari ce kawai ya magance ta.

Akintola yace Buhari ya dade yana yakar rashawa tun daga 1983 lokacin da ya kasance Shugaban kasa a mulkin soja.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa a yanzu haka Najeriya na samun cigaba ta fannin ababen more rayuwa fiye da yadda ta samu tun bayan samun yancin kai.

Hanyoyi, tsarin sufurin jirgin kasa na zamani, wanda a cewar kungiyar aka yasar a baya na samun kulawa a yanzu.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa tsarin asusun ajiya na bai daya da aka gabatar ya toshe kafar cin kudi.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa gwamnatin Buhari ta taimaka wajen biyan bashin albashin ma’aikata da fansho wanda ya zama biliyoyin nairori.

Kungiyar ta kara da cewa koda dai yan ta’addan Boko Haram sun kaddamar da hare-hare wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane a Kano da Abuja kafin 2015, anyi nasarar fatattakarsu daga arewa maso yamma tun lokacin.

KU KARANTA KUMA: Yancin kai: Sheikh Ahmed Gumi ya yi jawabi na musamman

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yan Najeriya tabbacin samun wutar lantarki mai dorewa kuma cikin sauki nan ba da jimawa ba.

Da yake magana a ranar bikin yanci na 59 a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, Shugaban kasar yace gwamnatinsa ta yanke shawarar kawo sauyi a ma’aikatar wutar lantarki.

Yayinda tallafin kudin lantarki a gwamnatin Buhari ya doshi naira triliyan 1.5 cikin shekaru biyar, wutar lantarki da ake ba gidajen yan Najeriya ya kasance kasa da megawatts 5,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel