Ku yi watsi da munanan dabi'u na rashin bin doka – Buhari ga yan Najeriya

Ku yi watsi da munanan dabi'u na rashin bin doka – Buhari ga yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga yan Najeriya da su yi watsi da munanan halayya sannan su cigaba da kasancewa masu bin doka a harkokinsu na yau da kullun.

A jawabinsa na kasa baki daya a ranar cikar Najeriya shekaru 59 da samun yancin kai a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, Shugaban kasar yace chanjin da yan Najeriya ke muradi zai zo ne daga dabi’u nagari.

“Za a iya isar da chanji ne kawai idan muka hada kai, a matsayinmu na mutane da kuma a matsayinmu na kasa. Ya zama dole dukkaninmu mu cigaba da jajircewa don cimma wannan manufa da chanji,” inji Shugaban kasar.

Ya tuna shawartan yan Najeriya shekaru hudu da suka gabata kan cewa akwai bukatar su dunga nuna hallayar kirki a koda yaushe.

Najeriya ta samu yancin kai daga Birtaniya a ranar 1 ga watan Oktoba, 1960.

KU KARANTA KUMA: Matsalar Najeriya bai da magani ta bangaren siyasa - Kungiyar CAN

A wani lamarin kuma, Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ibrahim Matane, ya gargadi 'yan Najeriya da su kauracewa zantuttuka na shaci fadi da kalaman nuna kiyayya domin tabbatar da zaman lafiya da kuma aminci a kasar.

Alhaji Matane ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da sa hannun mai magana da yawaunsa, Lawal Tanko, yayin murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yanci.

Babban jami'in gwamnatin ya nemi 'yan Najeriya da su dabi'antu da soyayyar juna, zaman lafiya, jituwa da kuma girmama junansu ba tare da nuna bambancin ra'ayi na addini, siyasa, ko kuma al'ada ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel