'Yan bindiga sun yi awon gaba da bindigu biyu bayan sun kashe dan sanda

'Yan bindiga sun yi awon gaba da bindigu biyu bayan sun kashe dan sanda

Rundunar 'yan sanda a jihar Abia ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga da ya zuwa yanzu ba a san ko su waye ba sun kai wa tawagar 'yan sanda hari ranar Juma'a inda suka kashe guda tare da raunata wani.

'Yan bindigar sun kai wa 'yan sandan uku hari ne yayin da suka fita sintiri. Daya daga cikin 'yan sandan ya tsira da lafiyarsa.

Kazalika, 'yan bindigar sun kashe direban motar da 'yan sandan suka yi amfani da ita wajen fita sintirin a yammacin ranar Juma'a.

An kai wa 'yan sandan hari ne yayin da suke tafiya a kan titin Ibadan da ke yankin Ndiegoro a garin Aba.

'Yan bindigar sun yi awon gaba da bindigu guda biyu bayan sun kai wa tawagar 'yan sandan hari.

'Yan sandan da aka kai wa harin na aiki ne a ofishin 'yan sanda na Ndiegoro.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun cafke dan gani kashenin Osinbajo a jihar Ondo, sun bayyana dalili

Wata majiya ta ce 'yan bindigar sun yi amfani da babbar wuka wajen ji wa daya daga cikin 'yan sandan mummunan rauni.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Abia, DSP Geoffrey Ogbonna, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ogbonno ya ce rundunar 'yan sanda sun kama mutane biyu da suke zargin na da alaka da kai harin.

"Jami'an 'yan sandan sun fita sintiri ne kamar yadda suka saba, amma sai wasu 'yan bindiga suka kai musu harin kwanton bauna tare da kashe daya daga cikinsu," a cewarsa.

Ya kara da cewa 'yan bindigar sun kwace bindigogin ne daga hannun jami'an 'yan sandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel