Matsalar Najeriya bai da magani ta bangaren siyasa - Kungiyar CAN

Matsalar Najeriya bai da magani ta bangaren siyasa - Kungiyar CAN

Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) tace ta gano cewa matsalar Najeriya ya fi karfin abunda za a iya magancewa a siyasance, inda ta bayyana cewa ya zama dole dukkanin yan Najeriya su kasance da hannu wajen magance matsalar.

Shugaban CAN, Samson Ayokunle, a sakon ranar damokradiyya, ya karfafawa yan Najeriya gwiwar addu’a ga Allah sannan su nemi taimakonsa a harkokin siyasar kasar domin Najeriya ta bunkasa ta kuma sake hawa turban girma.

Yace: "Ya kamata mu ajiye duk wani banbance-banbance da ke dukusar damu a bayanmu saboda Allah ya rigada ya kadarci kasancewarmu tare a kasa guda da ake kira Najeriya.

"Akwai bukatar mu karbi abubuwa a yadda suka zo sannan mu rungumi junanmu. Ya zaman dole muyi aiki domin inganta rayuwar yan uwanmu maza da mata. Yanzun ne lokacin bunkasa Najeriya a matsayin kasa ta hanyar hada kai da fata."

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya za su samu wutar lantarki mai dorewa nan ba da jimawa ba - Buhari

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Buhari a ranar Talata yayin gabatar da jawaban sa na zagayowar ranar samun 'yan kan da Najeriya tayi shekaru 59 da suka gabata, ya sake zargin gwamnatocin baya da sakaci wanda a cewarsa ya gurgunta tattalin arzikin kasar.

Ana iya tuna cewa a shekarar 2017 da ta gabata ne shugaban kasa Buhari ya bayyana farin cikin sa da cewa, tattalin arzikin kasar nan ya fara gyaruwa bayan wata ganawa da tsohuwar ministan Kudi ministar kudi, Kemi Adeosun, tsohon ministan kasafin Kudi da tsare-tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel