Yanzu-yanzu: Bayan dawowa daga Amurka, Buhari zai tafi kasar Afrika ta kudu gobe

Yanzu-yanzu: Bayan dawowa daga Amurka, Buhari zai tafi kasar Afrika ta kudu gobe

Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Afrika ta kudu a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2019 kan al'amarin kin jin bakin fata da ke addabi kasar Afrika ta kudu a makonnin bayan.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan ne da ranan nan a jawabin da ya saki inda yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari zai tashin ranar Laraba daga Abuja domin kai ziyarar kwanaki uku kasar Afrika ta kudu sakamakon goron gayyatar da shugaban kasa Cyril Ramaphosa, domin tattaunawa kan jin dadin yan Najeriya da zaman lafiyarsu a kasar."

"Wannan ziyara ya biyo bayan rikicin kin jinin bakin fata da ya faru da kuma kwashe yan Najeriya daga kasar."

Shugaba Buhari zai tafi tare da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano, gwamna Simon Lalong na Plateau da gwamna David Umahi na Ebonyi.

Daga cikin ministoci akwai ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama; ministan tsaro, Bashir Magashi; ministan lantarki, Saleh Mamman; ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; da ministan ma'adinai, Olamilekan Adegbite.

Sauran ministocin sune ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi da karamar ministar masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Mariam Katagum.

Hakazalika akwai NSA Babagana Munguno, dirakta janar na hukumar NIA, Ahmed Rufai da shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel