Yan Najeriya za su samu wutar lantarki mai dorewa nan ba da jimawa ba - Buhari

Yan Najeriya za su samu wutar lantarki mai dorewa nan ba da jimawa ba - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yan Najeriya tabbacin samun wutar lantarki mai dorewa kuma cikin sauki nan ba da jimawa ba.

Da yake magana a ranar bikin yanci na 59 a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, Shugaban kasar yace gwamnatinsa ta yanke shawarar kawo sauyi a ma’aikatar wutar lantarki.

Yayinda tallafin kudin lantarki a gwamnatin Buhari ya doshi naira triliyan 1.5 cikin shekaru biyar, wutar lantarki da ake ba gidajen yan Najeriya ya kasance kasa da megawatts 5,000.

“Muna shirin sauya harkokin ma’aikatar wutar lantarki. A watan Agusta na wannan shekarar, Mun kaddamar da shirin Shugaban kasa akan wutar lantarki domin zamanantar da kasar a rukuni uku: farawa daga 5 Gigawatts zuwa 7 Gigawatts, sai 11 Gigawatts a 2023, sannan daga karshe 25 Gigawatts bayan,” inji Buhari.

KU KARANTA KUMA: 'Yancin kai: Mun ba Iyayeyn gidanmu kunya - Tsohon 'Dan siyasar Arewa

A halin da ake ciki, shugaban kasar yace jagoranci nagari da bunkasar tattalin arziki ba za su tabbata ba tare da zaman lafiya, ingataccen tsaro da kuma aminci a kasa. Yace dole ne a yabawa dakarun sojin Najeriya da ke ci gaba da sadaukar da rayukansu domin kare martabar kasar nan wajen yakar kungiyar masu tayar da kayar ta Boko Haram a tsawon shekaru hudu da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel