Ganduje vs Abba: An karfafa tsaro a cikin birnin Kano yayinda ake kotu zata yanke hukunci gobe

Ganduje vs Abba: An karfafa tsaro a cikin birnin Kano yayinda ake kotu zata yanke hukunci gobe

An ga tulin jami'an tsaro a cikin kwaryar birnin Kano da ranan nan yayinda yake shirye-shiryen yanke hukunci tsakanin gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da abokin hamayyarsa, Abba Kabir Yusuf, Daily Nigerian ta bada rahoto.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Kotun zaben gwamnan jihar Kano ta zabi ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2019 domin yanke hukunci kan shari'ar da jam'iyyar PDP da dan takararta, Abba Yusuf, suka shigar kan gwamna Abdullahi Umar Ganduje na kalubalantar sakamakon zaben 9 ga Maris 2019.

Kotu ta sanar da wannan ne ta hanyar tura sakon waya ga jam'iyyun biyu. Sakataren kotun ne ya aika sakonnin.

A ranar 18 ga Satumba - INEC, APC, da Ganduje sun kammala muhawara da lauyoyin PDP da Abba Kabir Yusuf.

Lauyan INEC, Ahmed Raji SAN, yayin fashin baki kan al'amarin inda ya ce an baiwa jam'iyyar PDP da Abba Kabir daman bayyana sahihan takardun shaida a kotu amma yawancin takardun shaidun ba sahihai bane, saboda haka, ya bukaci kotu tayi watsi da karar.

A jawabin lauyan gwamnan, Offiong Offiong (SAN), ya ce jam'iyyar PDP ta gaza gabatar da sakamakon da ta tattara da kanta amma ta dogara kan sakamakon da hukumar INEC ta sanar, saboda haka, kotu tayi watsi da karar.

KU KARANTA: Dan sanda ya bindige abokiyar aikinsa har lahira

A bangaren lauyan APC kuwa, Alex Izinyon SAN, ya ce jam'iyyar PDP da Abba Kabir sun yi zargin cewa an saba doka wajen soke sakamakon zaben akwatunan zabe 207 amma basu gabatar da hujjoji akai ba. Saboda haka, ya bukaci kotu tayi watsi da karar.

Amma a bangaren lauyan PDP da Abba, Kanu Agabi SAN, ya ce babbar hujjarsu itace Abba Kabir ne ya lashe zaben zagayen farko a ranar 9 ga Maris 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel