Innalillahi: 'Yan sanda sun ceto mata 19 da tsohon ciki a wani gida da ake dirka musu ciki idan sun haihu a sayar da jariran

Innalillahi: 'Yan sanda sun ceto mata 19 da tsohon ciki a wani gida da ake dirka musu ciki idan sun haihu a sayar da jariran

- Hukumar 'yan sandan Najeriya sunyi nasarar ceto wasu mata guda goma sha tara

- An ceto matan ne a jihohin Akwa Ibom, Anambra, Abia, Imo, Rivers da kuma Cross Rivers

- An ceto a wasu gidaje ne da ake amfani dasu ana yi musu ciki idan sun haihu a sayar da jariran

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta sanar da yadda ta ceto wasu mata guda goma sha tara, wadanda suke dauke da tsohon ciki, a wani katafaren gida da maza ke zuwa su dirka musu ciki, bayan sun haihu kuma sai a sayar da jariran.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Ekana ya bayyanawa manema labarai cewa sun gano gidan ne a unguwar Iyawale, a cikin yankin Ikotun. Sannan ya kara da cewa matan da aka samu a gidan daga kan mai shekaru 15 zuwa 28 ne.

Ekana ya kara da cewa an ceto matan ne daga jihohin Akwa Ibom, Anambra, Abia, Imo, Rivers, da kuma jihar Cross Rivers, inda aka kai su jihar Legas domin a sama musu aikin yi da zasu dogara da kansu.

KU KARANTA: Mahaifina na lalata dani tun ina 'yar shekara 18, yanzu haka 'ya'yana guda biyu duk na shi ne - Matar aure ta tona asiri

Matar da take dillanci akan wannan lamari mai suna Madam Oluchi ta ranta ana kare, amma kuma an kama wasu daga cikin yaranta guda biyu masu suna Happiness Ukwuoma da Aherifat Ipaye.

Bincike ya bayyana cewa mutanen suna sayar da yaro jariri akan kudi naira dubu dari hudu (N400,000) jaririya kuma akan kudi naira dubu dari uku (N300,000).

Sannan an gano wasu kananan yara guda hudu da aka riga aka sayar da su.

Yanzu haka dai za a mika su zuwa kotu da zarar an kammala bincike akan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel