Dan sanda ya bindige abokiyar aikinsa har lahira

Dan sanda ya bindige abokiyar aikinsa har lahira

Wani jami'in dan sanda mai aiki a garin Asaba ya harbe abokiyar aikinsa har lahira a birnin jihar Delta, Asaba. Punch ta bada rahoto.

An tattaro labarin cewa wannan mumunan abu ya faru ne a ranar Asabar yayinda ake rusa wasu gidaje a unguwar Bonsaac da jami'an gwamnatin jihar keyi tare da jami'an tsaro.

Ana cikin gudanar da rusau, sai mata yan kasuwan suka tayar da tarzoma kan rusa musu gine-gine.

Wani mai idon shaida ya bayyana cewa daya daga cikin yan sandan ne ya harba bindiga ya kashe abokiyar aikinsa yar sanda ta baya bisa kuskure.

A yanzu, an garkame dan sandan da yayi kisan a sashen binciken hukumar.

Majiya ya bayyana cewa an garzaya da yar sandan asibitin FMC Asaba inda aka tabbatar da cewa ta rigamu gidan gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel