Buhari yayi kashedi ga hukumar Kwastam, FIRS da DPR a kan kudaden shiga

Buhari yayi kashedi ga hukumar Kwastam, FIRS da DPR a kan kudaden shiga

Shugaba Muhammadu Buhari yayi kashedi ga hukumonin da ke kawowa gwamnati kudaden shiga inda ya ce idan suka gagara kawo abinda aka shata masu za su fuskanci hukunci matsananci.

Shugaban kasan yayi wannan maganar ne a yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya game da ranar murnar cika shekaru 59 da samun ‘yancin kan kasar.

KU KARANTA:Ku bai wa Buhari hadin kai domin cika burinsa na ‘Next Level’, sakon Wamakko ga ‘yan Najeriya

Daga cikin hukumomin da wannan hukuncin zai shafa sun hada da Hukumar hana fasa kwauri ta Kwastam, FIRS, DPR da dai sauransu.

“Kokarin da muke cigaba da yi na samar da tattalin arziki mai inganci kuma yalwatacce shi ne dalilin da yasa muka hade ma’aikatar kudi da kuma kasafi ta kasa wurin guda.” Inji Buhari.

“Wadannan ma’aikatun guda biyu su ne ke da alhakin kula da duk wani shige da fice da kudade a gwamnatinmu. Ma’aikatun ne ke kula da kudaden shiga da kuma kasuwanci musamman ga masu kananan sana’o’i.

“A don haka ya zama wajibi mu sanya ido ga hukumomin dake tarawa kasar nan kudaden shiga, ta yadda zai kasance komi na tafiya yadda ya kamata. Amma kuma idan muka samu akasin hakan daga wata hukuma to hakika za ta fuskanci hukunci.

“Muradi dai a nan shi ne ya kasance ko wace hukuma ta iya kawo abinda aka yanke mata domin a matsayin kudaden shiga da ya kamata ta kawo.” Inji Shugaban kasa.

Haka zalika, Shugaban kasan ya bayyana cewa ma’aikatar kudi da kasafin kasa na musamman ta fitar da kudi biliyan N600 domin yin wasu manyan ayyukan raya kasa cikin watanni uku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel