Singham, tsohon kwamishina ya samu mukami a gwamnatin APC

Singham, tsohon kwamishina ya samu mukami a gwamnatin APC

- Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ba bawa tsohon kwamishinan 'yan sandan Kano, Mohammed Wakili, mukami

- Ismaila Misilli, kakakin gwamnan jihar Gombe, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin

- Wakili ya shiga bakin jama'a ne saboda jazircewarsa a kan aiki da kuma rashin tsoro, musamman rawar da ya taka yayin zaben gwamna a jihar Kano

Muhamnadu Inuwa Yahaya, gwamnan jihar Gombe, ya amince da nadin tsohon kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Mohammed Wakili, a matsayin mai bashi shawara a kan harkokin tsaro.

Gwamnan ya nada Wakili ne tare da sauran wasu hadimai guda biyar.

A cikin sanarwar da Ismaila Uba Misilli, kakakin gwamna Yahaya, ya ce gwamnan ya aika sunayen mutane 18 da yake son nada wa kwamishinoni zuwa majalisar dokokin jihar Gombe.

Misili ya ce nadin tsohon kwamishina Wakili da sauran hadimai biyar zai fara aiki nan take.

DUBA WANNAN: Kishi: Wani dattijo mai shekaru 60 ya kashe matarsa sannan ya kashe kansa

Wakili ya shiga bakin jama'a ne saboda jazircewarsa a kan aiki da kuma rashin tsoro, musamman rawar da ya taka yayin zaben gwamna a jihar Kano.

Tsohon kwamishinan ya taba kama mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, da kwamishinan kananan hukumomin jihar, Murtala Sule Garo, bayan sun yi kutse cikin cibiyar tattatara sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa tare da haddasa rikici.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel