Buhari ya umarci sakin N600bn don aiwatar da manyan aiyukan watanni 3 masu zuwa

Buhari ya umarci sakin N600bn don aiwatar da manyan aiyukan watanni 3 masu zuwa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ma'aikatar kudi, kasafi da tsari da ta saki naira biliyan 600 don manyan aiyuka a watanni 3 masu zuwa

- Shugaban kasar ya bada umarnin ne a yayin da ya gabatar da jawabinsa na murnar zagayowar ranar samun yancin Najeriya karo na 59

- Ya kara da bayyana cewa, mulkinsa na kokarin fadada tattalin arzikin kasar nan tare da fadada hanyoyin kudin shiga

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ga umarci ma'aikatar kudi, kasafi da tsari akan ta sakin naira biliyan 600 don manyan aiyuka a watanni 3 masu zuwa.

Shugaban kasar ya bada umarnin ne a yayin da ya gabatar da jawabinsa na murnar zagayowar ranar samu yancin Najeriya karo na 59 a Abuja.

KU KARANTA: Rundunar-sojin-najeriya-ta-kama-wani-mutum-da-zargi-da-kaiwa-yan-boko-haram-kayan-aiki

Ya ce umarnin ya biyo bayan bukatar mulkinsa na ganin ta habaka bangaren hannayen jari a kasar nan.

Kamar yadda ya ce, tabbatar da kasafin kudi na shekarar 2019, wanda aka aminta da shi a watan Yuni, 2019, zai tabbatar da cewa aiyukan da aka fi bukata sun kammalu.

Ya kara bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta saki naira tiriliyan 1.74 don aiwatar da manyan aiyuka a shekarar 2018.

"Ta wannan bangaren, muna karfafa saka hannayen jari a manyan bangarori. A shekarar da ta gabata, kudaden manyan aiyuka an sakesu ne bayan amincewar majalisa a watan Yuni na 2008." in ji shugaban.

"Hakazalika, zuwa ranar 20 ga watan Yuni na shekarar nan, an saki naira tiriliyan 1.74 don manyan aiyukan 2018," in ji shi.

Shugaban kasar ya kara da cewa, "A kokarinmu na fadada tattalin arzikin kasar nan, muna kuma maida hankali wajen ganin kudin shiga ta bangaren mai da iskar gas ya karu,"

"Za mu yi aiki da mahukunta wajen tabbatar da gyara dokar masana'antar man fetur don tabbatar da gwamnatin ta samu kaso mai tsoka na kudin shiga tare da bada kwarin guiwa ga bangarorin da ba na gwamnati ba," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel