Wani tsohon manajan banki ya daukaka kara akan kwace masa N9.08bn da kotu tayi

Wani tsohon manajan banki ya daukaka kara akan kwace masa N9.08bn da kotu tayi

- Tsohon manajan banki, Dauda Lawal, ya bukaci kotun daukaka kara da ke Legas da ta umarci gwamnatin tarayya ta dawo masa da kudinsa

- Kotu ta yanke hukuncin kwace kudin tare da mikasu ga gwamnatin tarayya ne bayan da ta gamsu da bayanan EFCC

- EFCC ta zargi cewa an wafto kudaden ne daga taskar matatar man fetur ta kasa wato NNPC a lokacin da Diezani Alison-Madueke ke ministar man fetur

Tsohon manajan banki, Dauda Lawal, ya bukaci kotun daukaka kara da ke Legas da ta umarci gwamnatin tarayya ta dawo masa da naira biliyan 9.08 da ta kwace a ranar 16 ga watan Fabrairu na 2017.

Lawal ya ce, babbar kotun tarayyar da ke Legas din da ta bada umarnin kwace kudaden bata da damar yin hakan a shari'ance.

Kamar yadda hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta sanar,an kwace naira biliyan 34 da suke da alaka da tsohuwar ministar man fetur, Diezan Alison-Madueke.

KU KARANTA: Rundunar-sojin-najeriya-ta-kama-wani-mutum-da-zargi-da-kaiwa-yan-boko-haram-kayan-aiki

EFCC ta zargi cewa, tsohuwar ministar da wasu sun hada kai wajen satar kudin ne daga matatar man fetur ta kasa, NNPC inda suka zuba su a bankuna 3.

A ranar 16 ga watan Fabrairu, 2017, mai shari'a Muslim Hassan, ya bada umarnin kwace kudin saboda babu wanda ya bayyana a matsayin halastaccen mai su.

Mai shari'ar ya ce, ya gamsu da ikirarin EFCC na cewa an samu kudin ne ba ta halatacciyar hanya ba.

Lawal ne ya mika daukaka karar inda EFCC ce wacce ake kara.

Mai daukaka karar ya samu wakilcin lauyansa, P.IN Ikwueto, inda Kufre Uduak ya wakilci EFCC.

Bayan da aka gabatar da shari'ar a ranar 29 ga watan Satumba, kotun ta dage sauraron karar bayan da ta sanar da bangarorin biyu cewa zata sanar musu da ranar sauraron shari'ar.

A daukaka karar, Lawal ya ce akwai kuskure a hukuncin.

Ya roki kotun abubuwa hudu da suka hada da: "Bukatar soke hukuncin ranar 16 ga watan Fabariru, 2017, bukatar soke hukuncin da aka yanke lokacin yana tsare, bukatar dawo masa da N9.08."

Kamar yadda ya daukaka karar, Lawal ya ce kudin da aka kwace ba a samesu a wajensa ba kamar yadda sashi na 17 na laifukan damfara ya tanadar.

Kamar yadda ya ce, iyalansa da abokan arziki ne suka samo bashin kudaden suka biya bayan yana tsare a wajen EFCC suka kuma mikawa gwamnati.

Ya kara da cewa, bai samu damar daukaka kara ba saboda bincikarsa da kuma tsaresa da EFCC ta yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel