Najeriya na cikin hadari saboda sabawa yarjejiniya da ta kulla da wasu kamfanoni 11 a duniya

Najeriya na cikin hadari saboda sabawa yarjejiniya da ta kulla da wasu kamfanoni 11 a duniya

Masana sun ce tattalin arzikin Najeriya zai iya durkushewa matukar gwamnatin kasar ta sadaukar da kadarorinta ga wani kamfanin iskar gas na tsibirin Ireland mai suna Process & Industrial Development Ltd, P&ID.

Wata kotun kasar Birtaniya ce dai ta bai wa Najeriya umarnin biyan kamfanin P&ID diyyar fiye da dala biliyan 9 sanadiyar sabawa wata yarjejeniyar samar da iskar da bangarori biyu suka kulla.

Tun a farkon watan Agustan da ya gabata ne, wata kotun London ta bai wa kamfanin P&ID, damar rike kadarorin Najeriya kwatankwacin wannan kudi, a matsayin diyya saboda saba wata yarjejeniya da suka kulla ta samar da iskar gas, lamarin da ministan shari'a na kasar, Abubakar Malami, ya ce za su kalubalanci hukuncin ta hanyar daukar duk wani mataki da ya dace.

A wani rahoto da jaridar The Nation ta ruwaito, a halin yanzu bincike ya tabbatar da cewa akwai kimanin kamfanoni 11 da ke kirdadon wannan dambarwa ta kamfanin P&ID ta lafa gabanin su huro ta su wutar sanadiyar sabawa yarjejeniyar da gwamnatin Najeriya ta kulla a tsakaninta da su.

KARANTA KUMA: Masu arziki a Najeriya za su sha wahala idan tattalin arzikin kasa ya ci gaba da fuskantar tasgaro

Tuni dai kamfanin kula da harkokin man fetur na kasa NNPC, ya nemi agajin hukumar yaki da rashawa ta Najeriya EFCC, da ta gaggauta fara gudanar da bincike kan yadda kamfanonin 11 suke da ruwa da tsaki da dambarwar kamfanin P&ID a yayin da suka daura damarar shigar da kararrakinsu a gaban kuliya.

Ga jerin sunayen kamfanonin 11 da kuma yarjejniyar da suka kulla da gwamnatin Najeriya

 • P&ID (Propane Dehydration (12-24 months) 88.198MMscf/d;
 • Octopol Energy Limited (LPG Extraction (12-15 months) 4.676MMscf/d, 3.039MMscf/d, 4.800MMscf/d, 2.100MMscf/d, 13.4MMscf/d;
 • Petrolog Oil &Gas Limited (CNG (9-24 months) 8.76MMscf/d, 20.600MMscf/d;
 • GFD Energy Nigeria Ltd (GFD) (2million MT Floating LNG) 5.7MMscf/d, 7.5MMscf/d, 2.2MMscf/d, 9.2MMscf/d;
 • Global Gas &refining Limited (GGRL) (LPG Extraction) 11.300MMscf/d, 12.398MMscf/d, 8.35MMscf/d.
 • Davubic Energy Development Comp. Ltd (LPG Extraction) 8.4MMscf/d, 21.516MMscf/d, 18.1MMscf/d;
 • Consortium of Drake Oil Limited & Partners (DOL) 7.42MMscf/d, 6.856MMscf/d, 14.564MMscf/d;
 • Tricity Oil Nigeria Ltd 1.266MMscf/d, 4.977MMscf/d, 2.026MMscf/d, 4.979MMscf/d, 3.777MMscf/d.
 • Colechurch International Ltd (LPG Extraction) 3.778MMscf/d, 3.335MMscf/d, 2.539MMscf/d, 2.071MMscf/d, 13.10MMscf/d, 1.000MMscf/d;
 • Eurafic Oil &Gas Ltd (LPG Extraction) 3.256MMscf/d, 5.075MMscf/d, 12.00MMscf/d;
 • Ibeto Group (LPG Extraction) 23.00MMscf/d, 34.3MMscf/d,
 • Borkir International Company Ltd. 26.558MMscf/d, 26.7MMscf/d.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel