Masu arziki a Najeriya za su sha wahala idan tattalin arzikin kasa ya ci gaba da fuskantar tasgaro

Masu arziki a Najeriya za su sha wahala idan tattalin arzikin kasa ya ci gaba da fuskantar tasgaro

Wani tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Farfesa Charles Soludo, ya ce masu arziki a kasar nan su zama cikin shirin fuskantar mawuyacin hali muddin ba a magance matsalar rashin aikin yi ba da kuma talauci da ya yi mafiya akasarin al'ummar kasar katutu.

Tsohon gwamnan ya ce masu arziki a Najeriya za su tsinci kawunansu cikin tsanani matukar ba a magance katutu na talauci da kuma rashin aikin yi da ya kai intaha a kasar.

Furucin Soludo na zuwa ne a ranar Talata yayin gabatar da jawabai a wani taro da wata cibiya ta Covenant Christian Centre ta dauki nauyi kan maudu'in yi wa tattalin arzikin kasa garambawul da aka gudanar cikin birnin Legas.

Ya yi babatu tare da bayyana damuwa dangane da yadda kasar nan ta gaza daina dogaro a kan arzikin man fetur duk yunkurin hakan da gwamnatocin baya suka yi.

KARANTA KUMA: Obasanjo da Jonathan sun jefa tattalin arzikin Najeriya cikin tasku - Buhari

Ya ce ya zama tilas Najeriya ta yi wa kanta karatun ta nutsu wajen fahimtar cewa makomar kowace kasa mai muradin taka mataki na ci gaba ta sauya akalar dogaro a kan albarkatun kasa wanda cin moriyarsu bai wuce na wani takaitaccen zango ba.

Ana iya tuna cewa, Farfesa Soludo na daya daga cikin mambobin majalisar bai wa shugaban kasa sharwawari a kan tattalin arziki da shugaba Buhari ya kafa makonni kadan da suka gabata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel