Obasanjo da Jonathan sun jefa tattalin arzikin Najeriya cikin tasku - Buhari

Obasanjo da Jonathan sun jefa tattalin arzikin Najeriya cikin tasku - Buhari

Bayan fiye da shekaru hudu da hawa kujerar mulki, ya zuwa yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari, na ci ga ba da zargin sakacin gwamnatocin baya da jefa tattalin arzikin kasar nan cikin tasku.

Gabanin hawansa kujerar mulki, kasar Najeriya ta kasance a karkashin jagorancin jam'iyyar PDP tun bayan komawar kasar kan tsarin dimokuradiyya. Olusegun Obasanjo, Umaru Musa Yar'Adu'a da kuma Goodluck Jonathan sun jagoranci kasar nan a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2015.

Buhari a ranar Talata yayin gabatar da jawaban sa na zagayowar ranar samun 'yan kan da Najeriya tayi shekaru 59 da suka gabata, ya sake zargin gwamnatocin baya da sakaci wanda a cewarsa ya gurgunta tattalin arzikin kasar.

Ana iya tuna cewa a shekarar 2017 da ta gabata ne shugaban kasa Buhari ya bayyana farin cikin sa da cewa, tattalin arzikin kasar nan ya fara gyaruwa bayan wata ganawa da tsohuwar ministan Kudi ministar kudi, Kemi Adeosun, tsohon ministan kasafin Kudi da tsare-tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.

KARANTA KUMA: Muhimman jawabai da Buhari yayi a bikin cika shekara 59 da samun 'yancin kan Najeriya

Hakazalika tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a wani rahoto da jaridar BBC Hausa ta wallafa a ranar 11 ga watan Janairun 2011, ya ce shugaba Buhari na matukar sakaci da tattalin arzikin kasar nan duk da irin koken da al'umma suke yi na fama da yunwa da kuma talauci.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel