Muhimman jawabai da Buhari yayi a bikin cika shekara 59 da samun 'yancin kan Najeriya

Muhimman jawabai da Buhari yayi a bikin cika shekara 59 da samun 'yancin kan Najeriya

A yau Talata, 1 ga watan Okotoba 2019, Najeriya ta ke murnar zagayowar ranar samun 'yancin kai daga hannun Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a ranar 1 ga watan Oktoba na 1960 wato shekaru 59 da suka gabata.

Da misalin karfe 7.00 na safiyar yau Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabai gidan talabiji din kasa inda ya jaddada kudirin gwamnatin sa na inganta jin dadi da kuma kare hakkin kowane dan kasar.

A wani rahoto da muka kalato daga karaf watsa labarai ta Channels TV, ga wasu muhimman zantuttuka da Buhari yayin gabatar da jawabansa na murnar zagayowar ranar samun 'yanci.

1. Shugaba Buhari ya ce sauyi ba zai taba tabbata matukar babu hadin kai a tsakanin al'umma. Dole ne kowa ya jajirce wajen cimma manufar tabbatar da magarcin sauyi a Najeriya.

2. Magarcin jagoranci da bunkasar tattalin arziki ba za su tabbata ba tare da zaman lafiya, ingataccen tsaro da kuma aminci a kasa. Dole ne a yabawa dakarun sojin Najeriya da ke ci gaba da sadaukar da rayukansu domin kare martabar kasar nan wajen yakar kungiyar masu tayar da kayar ta Boko Haram a tsawon shekaru hudu da suka gabata.

3. Dole ne mu ci gaba da tsayuwar daka wajen yakar tsageru masu kai hare-hare a yankunan Neja Delta da fashe butatan mai dake janyo wa kasa asarar dukiya mai tarin yawa.

4. Muna kuma sane da yadda miyagun laifuka ta yanar gizo ke ci gaba da karuwa a kasar nan da yaduwar kalaman nuna kiyayya da batanci musamman a zaurukan sada zumunta.

5. A yayin da muka sha alwashin bai wa kowane dan kasar hakkin sa gwargwadon tanadi na kundi tsarin mulkin kasa, za kuma mu sa kafar wando daya da masu yada kalaman kiyayya a kasar, domin babu inda tafarkin kiyayyar juna zai kai mu illla ga halaka.

6. Baya ga farfadowar tattalin arzikin kasa, muna ci gaba samun habakarsa a tsawon watanni 27 da suka gabata tun bayan ficewar mu daga matsi na tattalin arziki a shekarar 2017.

7. Aiki da lura gami da daukar izina daga kurakuran da muka tafka a baya na daya daga cikin mafifitan akidu da gwamnatin mu ta sanya a gaba musamman cin ribar arzikin man fetur da kasar ta ke da shi ta hanyar dace.

KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Neja ta gargadi 'yan Najeriya a kan kalaman nuna kiyayya

8. Za kuma mu jajirce wajen rage dogaro a kan arzikin man fetur wajen bijiro da hanyoyin samar da abun yi domin hana al'ummar kasa zaman kashe wando musamman matasan cikinta.

9. Ina mai jaddadawa 'yan Najeriya alwashin samar da dawwamammiyar wutar lantarki nan da wani lokaci takaitacce.

10. Za mu ci gaba da inganta shirye-shiryen mu na bai wa al'umma tallafi na abin dogaro da kai da kuma zage dantse wajen fatattakar annobar cin hanci da rashawa ta hanyar binciken diddigi da hukunta masu yi wa dukiyar talakawa ta'annati.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel