Ku bai wa Buhari hadin kai domin cika burinsa na ‘Next Level’, sakon Wamakko ga ‘yan Najeriya

Ku bai wa Buhari hadin kai domin cika burinsa na ‘Next Level’, sakon Wamakko ga ‘yan Najeriya

Shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan harkokin tsaro, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga ‘yan Najeriya da cewa su bai wa Shugaba Muhammadu Buhari hadin kai domin ya samu damar cikan burinsa na kai Najeriya zuwa ga mataki na gaba.

Wannan maganar na kunshe ne cikin jawabin sanatan na muranr cikan Najeriya shekaru 59 da samun ‘yancin kai.

KU KARANTA: Ranar ‘yanci 2019 : Sakon Shugaba Muhammadu Buhari ga ‘yan Najeriya

Sanatan wandan ke wailtar Sokoto ta Arewa a daren Litinin 30 ga watan Satumba, ya fadi a cikin wani zancensa da hadiminsa Bashir Rabe Mani ya fitar, "duk masu kaunar Najeriya basu da wata bukata da ta wuce ganin kasar ta cigaba."

A cewarsa, “Shugaban kasa na cigaba da fadi tashin ganin ya saita al’amuran Najeriya zuwa wani mataki na musmaman ta yadda ‘yan kasa za su amfana.”

A wani labari mai kama da wannan kuwa, zaku ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan Najeriya da cewa su cigaba da zama da juna cikin zaman lafiya da hadin kai domin ciyar da kasar nan gaba.

Shugaba Buhari ya yi wannan maganar ne a cikin jawabinsa na murnar cikan Najeriya shekara 59 da samun ‘yancin kai, inda ya fadi wasu matsalolin da gwamnatin ke fama da su a halin yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel