Ranar ‘yanci 2019 : Sakon Shugaba Muhammadu Buhari ga ‘yan Najeriya

Ranar ‘yanci 2019 : Sakon Shugaba Muhammadu Buhari ga ‘yan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari a safiyar yau Talata 1 ga watan Oktoba, 2019 ya yi kira ga ‘yan Najeriya na su hada hannuwansu tare da marawa gwamnati baya domin ciyar da kasar nan gaba.

A cikin jawabin da shugaban kasan yayi na murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun ‘yancin kai, ya ce: “Najeriya za ta farfado daga cikin halin da ta jima cikinsa na tsanani nan bada jimawa ba.”

KU KARANTA:Yancin kai: Sheikh Ahmed Gumi ya yi jawabi na musamman

Haka kuma Shugaban kasan yayi kira ga ‘yan Najeriya da cewa su kara hakuri kana kuma suyi amfani da hanyoyin da suka dace domin isarwa gwamnati da korafe-korafensu.

A cewarsa, “Mun fi mayar da hankalinmu yanzu a kan masu aikata muggan laifuka ta hanyoyin zamani wato masu amfani da yanar gizo. Akwai kuma masu yada labarai marasa tushe a shafukan sadarwa na zamani.

“Duk da cewa muna cigaba da mutunta kundin tsarin kasarmu wanda ya halarta ‘yancin fadin albarkacin baki ga ko wane dan kasa, amma kuma ba za mu zuba muna kallon wadansu tsirarun mutane na neman haddasa fitina a kasar ba.”

Shugaba Buhari ya kara da cewa: “Kiyayya da ganin kyashi ba komi take haifarwa ba in banda tabarbarewar kasa da kuma rashin cigaba. Ina da yakinin cewa akasarin ‘yan Najeriya sun fi sha’awar zaman lumana da kwanciyar hankali da juna.”

Bugu da kari, shugaban kasan ya ce kaddamar da kasafin kudin 2019 wanda aka yi a watan Yuni zai soma aiki cikin gaggawa domin ganin cewa an kammala ayyukan manya masu matukar amfani ga jama’ar kasar Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel