'Dan sanda ya bindige abokiyar aikinsa 'yar sanda har lahira

'Dan sanda ya bindige abokiyar aikinsa 'yar sanda har lahira

Wani abin bakin ciki ya faru a ranar Asabar 28 ga watan Satumba lokacin da wani dan sanda ya harbe abokiyar aikinsa mai shekaru 28 yayin da ma'aikatan hukumar muhalli na jihar Delta suka fara zanga-zanga kan rushe wasu gine-gine da aka yi ba bisa ka'ida ba a unguwar Bonsaac.

Dan sandan ya kashe abokiyar aikinsa ne cikin kuskure yayin da ya ke harbe-harbe domin tawartsa wasu mata 'yan kasuwa da ke cikin 'yan zanga-zangan. Tuni dai jami'an sashin binciken manyan laifuka sun tsare dan sandan bayan an tabbatar da cewa abokiyar aikinsa ta mutu.

Wata wanda abin ya faru a gabanta ta ce "Shugaban masu bayar da haya a Bonsaac, Mista Bidi ya dade yana musgunawa mata 'yan kasuwa yana son ya kore su daga inda suke kasuwanci bayan sun kafa tanti sun kuma suna biyan mai filin N2000 duk wata.

DUBA WANNAN: Kogi: Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana dan takarar da za ta jefa wa kuri'a

"A ranar Juma'a 26 ga watan Satumban 2019, mai filin tare da hadin bakin DPO din 'B' Division na 'yan sanda sun kawo babban mota domin rusa shagunnan inda ta tura 'yan sanda hudu domin su taya mai rusau aikinsa.

"Bayan rushe shagunansu duk da cewa baya janyo cinkosun motocci ko tare hanyar ruwa, matan sun bukaci a rushe shagunan da ke cikin harabar ma filin saboda tun farko ya fada musu cewa ma'aikatar muhalli ne ta bayar da umurnin yin aikin."

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Adeyinka Adeleke ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Litinin 30 ga watan Satumba inda ya ce har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

Ya ce, "Lamarin na hannun sashin binciken manyan laifuka a Asaba saboda haka muna sauraron rahoto daga wurinsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel