Badakalar N3.1bn: EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan PDP a kotu

Badakalar N3.1bn: EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan PDP a kotu

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati, EFCC a ranar Litinin ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam da kwamishinan kudi na gwamnatinsa, Omadachi Oklobi kan zargin almundahanar kudi naira biliyan 3.1.

Suswam wanda yanzu Sanata ne mai wakiltan Benue North East da wanda ake tuhumansu tare sun ce ba su amsa laifuka tara da ake tuhumansu ba da aka karanto musu a gaban Mai shari'a Okon Abang na kotun tarayya da ke Abuja.

Da farko an gurfanar da su gaban Mai shari'a Ahmed Mohammed duk da a Abuja a Nuwamban 2015 amma Mai shari'a Mohammed ya janye daga shari'ar a Yulin wannan shekarar.

DUBA WANNAN: Kogi: Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana dan takarar da za ta jefa wa kuri'a

Hakan ya sa aka bawa Mai shari'a Abang domin ya cigaba da sauraron shari'ar.

Kafin a gurfanar da shi a ranar Litinin, Mai shari'a Abang ya ki amincewa da wata bukata da wadanda ake tuhumar su kayi na neman canja alkalin shari'an.

Suswam, ta bakin lauyansa, Chinelo Ogbozor ya bukaci alkalin ya mayarwa Mai shari'a Mohammed takardun shari'an domin ya cigaba da sauraron karar.

A yayin da ya ke yanke hukunci, Mai shari'a Abang ya amince da bukatar da lauya mai shigar da kara, Leke Atolagbe ya gabatar na neman ya cigaba da sauraron shari'ar kuma ya bayar da umurnin gurfanar da wadanda akayi karar a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel