Yanzu nan: Jami’an DSS sun yi rubuti sun cafke Abdulrasheed Maina a otel

Yanzu nan: Jami’an DSS sun yi rubuti sun cafke Abdulrasheed Maina a otel

AbdulRasheed Maina wanda ya yi aiki a wani kwamiti na musamman domin gyara harkar fansho a Najeriya ya fada hannun jami’an tsaro masu fararen kaya na DSS bayan an dade ana nemansa.

Rahotanni na zuwa mana cewa Jami’an kasar sun damke Alhaji Maina ne a cikin wani otel a babban birnin tarayya Abuja. Wannan abu ya faru ne a Ranar Litinin, 30 ga Watan Satumban 2019.

Kamar yadda mu ka samu labari, DSS sun samu damar cafke AbdulRasheed Maina ne bayan ya shigo cikin Najeriya a sace. Kafin yanzu Maina ya na boye ne a Birnin Dubai da ke kasar UAE.

An soma rade-radin cewa za a mika tsohon jami’in gwamnatin tarayyar a gaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa kan zargin batar da wasu Biliyoyin kudi.

KU KARANTA: FG ta fadawa Duniya abin da ta karbe daga hannun Maina - Kotu

Ana zargin Maina da bada wasu kwangilolin bogi na Naira biliyan 2 a lokacin ya na kula da kwamitin yi wa harkar fansho garambawul a Najeriya. Tun 2015 ake neman hanyar kama Maina.

Dama jami’an tsaro sun dade su na bin dakon Maina inda su ka hada-kai domin ganin an yi ram da shi. Yanzu haka ya na can ana ta faman yi masa tambayoyi kafin a mika shi gaban hukuma.

Kakakin hukumar ta DSS masu fararen kaya, Peter Afunaya bai fitar da jawabi game da damke wanda ake zargin ba. An kuma yi kokarin tuntubar Dr. Afunaya a wayar salula, amma ya yi gum.

Kwanakin baya badakalar AbdulRasheed Maina ta yi kamari bayan da wasu manyan jami’an gwamnati su ka yi kutun-kutun su ka dawo da shi bakin aiki yayin da ake nemansa a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel