Sojoji sun kama 'yan kasashen waje 8 da ke yi wa Boko Haram aiki

Sojoji sun kama 'yan kasashen waje 8 da ke yi wa Boko Haram aiki

Dakarun sojojin Najeriya sun kama wani direban mota da bakin haure 7 a cikin mota da ake kyautata zaton suna yi wa kungiyar ISWAP da mayakan kungiyar ta'addan Boko Haram da ke titi Yola aiki ne.

The Punch ta ruwaito cewa sojojin sun kama wadanda ake zargin ne yayin da suke ratsawa da wani shingen bincike da sojojin suka kafa a titin. A halin yanzu sojojin sun iya ganu sunan direban Musa Ibrahim.

A cewar sanarwar da hedkwatan sojoji na Abuja ta fitar a ranar Litinin, an yi kamen ne tsakanin ranakun 25 zuwa 28 na watan Satumba bayan sojojin sun kama wani mai samar wa kungiyar ababen sufuri, Alhaji Kololi Modu a Ndollori a Maiduguri.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama wanda ya kashe mata da mijinta da diyarsu a Kano

Jami'in da ke kula da sadarwa na sojojin, Kwanel Aminu Iliyasa ya ce dakarun Operation Lafiya Dole, Operation Mesa da Swift Response za su cigaba da bincike da kama miyagun domin hana sakat musamman lokacin bukukuwan shekarar 2019.

Wani sashi na sakonsa ya ce, "Dakarun bataliya ta 231 da hadin gwiwan bataliyan 331 sun kama wani direban mota mai suna Musa Ibrahim da wasu fasinjoji bakwai da ake kyautata zaton bakin haure ne daga kasashen da ke makwabtaka da Najeriya. Ana kyautata zaton wadanda ake zargin suna da alaka da ISWAP.

"Kuma dai dakarun sojojin 7 Division Garrison yayin wani aikin hadin gwiwa da ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro sun kama wani gawurtaccen mai samar wa 'yan ta'adda kayayyaki, Alhaji Kolomi Modu a garin Ndollori na Ajilari a Maiduguri."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel