Hukumar EFCC na kara tuhumar wani tsohon gwamna da wasu laifuka

Hukumar EFCC na kara tuhumar wani tsohon gwamna da wasu laifuka

- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC tuhumar tsohon gwamnan jihad Filato, Jonah Jang da karin wasu laifukan

- Laifukan sun hada da waskar da kudaden tsaro na amfanin jihar zuwa biyan albashin ma'aikatan jihar sakamakon karbar kuwan biliyan uku da ya yi daga hukumar SUBEB

- Idan zamu tuna dai ana zargin tsohon gwamnan ne da laifuka 12 a da, a zaman kotun da aka yi jiya Litinin, laifukansa sun kai 17

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC, tana kara tuhumar tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang da wasu laifukan.

A ranar Litinin, shaida ta 12, Mary Anthony Bawa, ta sanar da mai shari'a Longji na babban kotun da ke zama a Jos cewa, bashin N2.079 da tsohon gwamnan ya karba don amfanin hukumar ilimi ta PLASUBEB ba a bi ta tsarin da ya dace ba.

Ana tuhumar Jang da laifuka 12 da suka hada da amfani da kujerarsa ta lokacin ba yadda ya dace ba, almubazzaranci da almundahanar kudade da zasu kai N10bn.

A zaman kotun da aka yi jiya Litinin, hukumar EFCC ta gyara tuhume-tuhumen har zuwa 17.

A zaman, Bawa, wacce shaida ce mai lamba 12 kuma ma'aikaciyar gwamnati ce a ofishin babban akawun jihar, karkashin ma'aikatar kudi, ta shaida cewa, "A matsayina na kwararriya a harkar kudi, hanyar da aka bi wajen karbar kudin ta taka doka. Kawai abinda na sani shi ne an turomin cewa an karba bashin N2.079bn."

KU KARANTA: Tsoffin-jami-gwamnatin-tarayya-na-cikin-tashin-hankali-akan-kwangilar-da-ta-jefa-najeriya-a-bashi

Kamar yadda ta sanar, "Bayan da na hau kujerata, abokan aikina sun nuna min cewa gwamnatin da ta shude ta ranci N2.079bn. Na kara fitar da wani bashin na N750,000,000 bayan wasika da ta iso gareni kuma na bi umarnin shugabana."

Ta kara da cewa, sakamakon bashin da ya kai kusana na biliyan uku da aka karba daga hukumar, an dakatar da gyaran makarantu, samar da bencina da tebura na makarantun firamare da sakandire na jihar da sauran aiyukan da suka rataya a wuyan hukumar.

"SUBEB ta kasa cigaba da aiyukanta saboda kudaden an waskar da su. Bayan nan an kara karbar wata N1bn itama a matsayin bashi amma miliyan 400 ce aka sakar mana. A don haka ne muka rasa kudin biyan albashin malamai wanda har akayi watanni hudu ba albashi saboda rashin kudi," in ji ta.

Yayin da lauya mai gabatar da kara, Rotimi Jacobs, ya jagoranci shaida ta 12, ta ce, "Kafin in bar SUBEB a watan Augusta 2015, rashin dawo da basussukan ya zama illa ga bangaren ilimi don duk aiyukan ba a iya aiwatar dasu."

Wani daga cikin karin laifukan tsohon gwamnan shi ne, a yayin da yake gwamnan jihar, a watan Maris na 2015, ya tura miliyan 900 na tsaro don biyan albashin malaman firamare na jihar wanda ya ci karo da sashi na 22, sakin layi na biyar na dokokin rashawa na 2000.

Lauyoyin wanda ake kara da suka samu jagorancin G. Pwajok, sun bukaci karin lokaci don duba karin laifukan tare da maida martani yadda ya dace.

Mai shari'a Longji ya dage sauraron karar zuwa 10 ga watan Oktoba, 2019 don cigaba da shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel