Rundunar sojin Najeriya ta kama wani mutum da take zargi da kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki

Rundunar sojin Najeriya ta kama wani mutum da take zargi da kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki

- Rundunar 'Operation Lafiya Dole' ta sojin Najeriya ta cafke wani mutum mai suna Samuel Chikwedum wanda take zargi da kaiwa 'yan ta'addan Boko Haram kayan aiki

- Sojin sun kama mutumin ne a garin Baga inda ya doshi yankin tafkin Chadi da wasu haramtattun kaya

- Shugaban runduna ta 7 ta sojin, Birgediya janar Aliyu Ibrahim ya sanar da cewa wanda ake zargin ya yi yunkurin bada cin hanci ga sojin, abinda Chikwedum ya musanta

Rundunar 'Operation Lafiya Dole' ta rundunar sojin Najeriya ta sanar da kama Samuel Chikwedum; wanda take zargi da samarwa 'yan ta'addan Boko Haram na jihar Borno da kayayyakin aiki.

Sojin sun kama Chikwedum ne yayin da yake tafiya zuwa garin Baga, inda ya doshi yankin tafkin Chadi da kayayyakin da basu dace ba.

Kamar yadda sojin suka sanar, bayan sojin sun cafkesa, an lalata kayansa da abun hawansa.

KU KARANTA: Tarihin-kadan-daga-cikin-jaruman-kannywood-masu-tasowa

Babban soja mai kula da runduna ta 7, Birgediya janar Aliyu Ibrahim, ya ce wanda ake zargin ya yi yunkurin bada cin hanci ga sojin da suka tsaresa don tambayarsa.

Amma kuma Chikwedum ya musanta zargin nan inda ya jaddada cewa shi kasuwancinsa halastacce ne kuma bai yi yunkurin bada hanci ba yayin da aka kamasa.

"Babu wanda na yi yunkurin baiwa hanci. Abinda na sanar dasu shine halin da kasar nan ke ciki inda gwamnatin kasar bata bin umarnin kotu," a cewarsa.

A don haka ne ya bukaci a sauraresa don tantance me ya kaisa yankin.

Idan zamu tuna, shekaru sun kai goma ko fiya da 'yan ta'addan Boko Haram suka addabi yankin arewa maso gabas din kasar nan.

'Yan ta'addan basu tsaya a yankin kadai ba, sun fara gangaro yankin arewa maso yamma na kasar nan inda suka dinga das abubuwa masu fashewa.

An kuwa samu irin wannan ta'asar har a birnin tarayyar Najeriyar kasar nan.

Gwamnatin Najeriya kuwa tana kokari wajen kawo karshen rashin tsaron amma abin ya ci tura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel