Kishi: Wani dattijo mai shekaru 60 ya kashe matarsa sannan ya kashe kansa

Kishi: Wani dattijo mai shekaru 60 ya kashe matarsa sannan ya kashe kansa

Rafiu Irawo, wani mutum mai shekaru 60 da ke zaune a Ile-Ife ta jihar Osun, ya kashe kansa bayan ya kashe matarsa, Funke, bisa zarginta da cin amanarsa da wani mutum a sirrance.

Lamarin ya faru ne ranar Juma'a a unguwar Alakowe da ke Ile-Ife amma har yanzu jama'ar yankin na zaune cikin rudani.

Wasu fusatattun matasa sun kone gidan Rafiu saboda jin haushin ya kashe matarsa.

Jami'an 'yan sanda na ofishin Osu sun kama dattijon bayan ya kashe matarsa, sai dai basu san cewa ya hadiyi wata guba da ta yi sanadiyar mutuwarsa a caji ofis.

Rafiu, mai sana'ar sayar da giya, yana da mata uku kafin daga bisani ya auri Funke a matsayin ta hudu.

DUBA WANNAN: Na shafe shekaru 13 ina lalata da mijin 'yar uwata, zunubin ya ishen haka - Budurwa

Rahotanni sun bayyana cewa marigayiyar ta haifi 'ya'ya biyu tare da tsohon mijinta kafin ta auri Rafiu, kuma tana aiki ne a shagonsa na sayar.

Funke da Rafiu sun haifi yaro guda daya, wanda yanzu ya zama maraya.

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Osun, Folasade Odoro, ya ce har yanzu suna gudanar da bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel