Ambaliyar ruwa: NEMA ta gargadi mazauna wasu garuruwa 4 da su yi gaggawan tashi

Ambaliyar ruwa: NEMA ta gargadi mazauna wasu garuruwa 4 da su yi gaggawan tashi

Hukumar da ke bayar da agajin gaggawa (NEMA), ta hankaltar da mazauna wasu garuruwa hudu da ke Jihar Imo akan su gaggauta ficewa ba tare da bata lokaci ba.

Tayi gargadin ne ta hannun shugaban hukumar mai kula da jihohin Imo da Abia, Evan Ugoh.

A cewarsa, sakamakon gargadin da hukumar nazarin yanayin ambaliya ta NIMET ta yi, akwai yiwuwar barkewar ambaliya a garuruwan Eziorsu, Atiaofu, Orsuenbodo da kuma Ossemotto.

Ya kuma ja kunnen mazauna Orashi da ke gefen Kogin Neja cewa su ma a bisa yadda yanayi ya nuna, bai kamata su kara kwantawa barci a garin ba.

Daga kashe yashawarci masu gina gidaje su daina gini a hanyar magudanar ruwa, a cewarsa hakan na kawo matsala mai gidan dama mutane baki daya.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai gabatar da jawabi ga 'yan kasa a ranar 1 ga watan Oktoba

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya ce kokarin dakarun rundunar soji kadai ba zai kawo karshen aiyukan ta'addanci da 'yan ta'adda ba tare da bayyana cewa dole sai kungiyoyin addini na kasa sun shiga sahun gaba, saboda yakin na addini ne.

Shugaban rundunar sojin ya ce akwai bukatar kungiyoyin addini su shigo cikin lamarin yaki da ta'addanci saboda 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram da ISWAP na kafa hujja da addini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel