Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kai hari kan sojoji a Borno

Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kai hari kan sojoji a Borno

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar yan ta’addan Boko Haram ta hallaka akalla mutane tara a wani hari da ta kaddamar kan garin Gubio da ke jihar Borno.

Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya rahoto cewa an kai harin ne a yammacin ranar Lahadi, 29 ga watan Satumba, inda yan ta’addan suka dauke lokaci mai tsawo suna kaddamar da harin.

Reauter a ranar Litinin, 30 ga watan Satumba, ta kuma rahoto cewa kungiyar IS ta fitar da ikrarin cewa ta kai harin sannan kuma ta kashe tare da jikkata sojoji da dama.

Rundunar soji da ke aikin Operation Lafiya Dole ta tabbatar da kai harin, sai dai ta ce ba kamar yadda ake bayar da rahoto lamarin yake ba.

Birgedia Janar Adesino Olusegun wanda shi ne shugaban rundunar Lafiya Dole din ya bayyana cewa ya ziyarci garin Gubio da yammacin ranar Litinin din nan, inda ya ce dakarunsu sun dakile harin na Boko Haram na ranar Lahadi.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai gabatar da jawabi ga 'yan kasa a ranar 1 ga watan Oktoba

Ya kara da cewa sojojin nasu sun samu nasarar fatattakar 'yan Boko Haram tare da kwace makamansu bayan kashe wasu daga cikinsu duk da cewa bai fadi adadinsu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel