Buhari zai gabatar da jawabi ga 'yan kasa a ranar 1 ga watan Oktoba

Buhari zai gabatar da jawabi ga 'yan kasa a ranar 1 ga watan Oktoba

Daga cikin shirye shiryen bikin ranar cikar Najeriya shekaru 59 da samun yancinta, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabi ga al’umman kasar baki daya a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba.

A cewar wata sanarwa daga kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, Buhari zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7:00 na safe.

Mallam Garba wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook yace ana bukata tashoshin talbishan, gidajen radiyo tare da cibiyoyin yada labarai duk su sadu da Babbar cibiyoyin sadarwa na kasa wato Nigeria Television Authority da Radio Nigeria don samun jawabin.

A wani lamari makamancin haka, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya taya Najeriya murnar cika shekaru 59 da samun 'yancin kai.

Trump ya aiko sakon taya murnan ne a cikin wata wasika da ya aiko wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Yaki da ta'addanci: Ba zamu iya mu kadai ba, sai Malaman addini sun agaza - Buratai

Ofishin jakadancin kasar Amurka a Najeriya ne ya wallafa sakon shugaba Trump. A cikin sakon, shugaban na Amurka ya yi magana a kan hadin kan da ke tsakanin Najeriya da Amurka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel