Trump ya rubuto wa Buhari wasika

Trump ya rubuto wa Buhari wasika

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya taya Najeriya murnar cika shekaru 59 da samun 'yancin kai.

Trump ya aiko sakon taya murnan ne a cikin wata wasika da ya aiko wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ofishin jakadancin kasar Amurka a Najeriya ne ya wallafa sakon shugaba Trump.

A cikin sakon, shugaban na Amurka ya yi magana a kan hadin kan da ke tsakanin Najeriya da Amurka.

"Mu abokan juna ne ta fuskar yaki da ta'addanci, kuma mu na bukatar ganin an murkushe kungiyar Boko Haram da kuma korar wakilan kungiyar ISIS daga yankin nahiyar Afrika maso yamma," kamar yadda Trump ya rubuta.

Wani bangare na wasikar ya ce, "amadadin mutanen kasar Amurka, ina mika sakon taya Najeriya murnar cika sheakaru 59 da samun 'yancin kai.

"Najeriya na daga cikin manyan kawayen Amurka a nahiyar Afrika. Mun dade mu na aiki tare wajen inganta tattalin arzikin kasashen mu. Mu abokan juna ne ta fuskar yaki da ta'addanci, kuma mu na bukatar ganin an murkushe kungiyar Boko Haram da kuma korar wakilan kungiyar ISIS daga yankin nahiyar Afrika maso yamma."

DUBA WANNAN: Gwamnatin Swiss ta kwace motoci 25 a hannun dan shugaban kasa kuma mataimakin mahaifinsa a kasar Afrika

Kazalika, Trump ya bayyana cewa kasar Amurka a shirye take koda yaushe ta taimaki Najeriya da sauran kasashen Afrika wajen ganin rayuwar mutanensu ta inganta.

"Ina mai farin cikin kulluwar alaka tsakanin mataimakan mu tun bayan haduwar mu a cikin shekarar da ta gabata, akwai dogon tarihi na hadin kai a tsakanin Najeriya da kasar Amurka.

"Ina yi wa mutanen Najeriya fatan alheri a wannan lokaci da kasar su ta samun karin shekara guda da samun 'yanci," a cewar Trump.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel