Ka cika alkawaran zaben da ka dauka – Buhari ga gwamnan Osun

Ka cika alkawaran zaben da ka dauka – Buhari ga gwamnan Osun

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun, da ya aiwatar da shirye shiryen jam’iyyar All Progressives Congress da kuma cika alkawaran da yayi ma masu zabe.

Shugaban Kasa Buhari ya bayar da shawaran ne jiya Lahadi, 29 ga watan Satumba, a wani jawabin taya murna da hadimin shugaban kasa Femi Adesina ya mika ga Oyetola, a bikin zagayowa ranar haihuwarsa karo na 65.

Shugaban kasar ya yabi gwamnan bisa kudurinsa na inganta wadatattun kayayyakin more rayuwa, hidima ga jama’a, cigaban al’umma da na jihar baki daya.

Ya bukace shi da yayi amfani da taron bikin ranar haihuwarsa karo na 65 a matsayin damar sake sadaukar da kansa don gudanar da hidima ga Allah da Al’umma.

KU KARANTA KUMA: Nigeria@59: Najeriya ba lafiya - Atiku Abubakar ya yi korafi

Buhari ya sadu da iyalen Oyetola, abokansa da mutanen arziki a mika fatan alkhairi da karin lafiya, daukakan basira da kuma karin shekarun masu muhimmanci da kuma shugabanci mai hangen nisa ga mutanen kirkin jihar Osun.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel