Yaki da ta'addanci: Ba zamu iya mu kadai ba, sai Malaman addini sun agaza - Buratai

Yaki da ta'addanci: Ba zamu iya mu kadai ba, sai Malaman addini sun agaza - Buratai

Shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya ce kokarin dakarun rundunar soji kadai ba zai kawo karshen aiyukan ta'addanci da 'yan ta'adda ba tare da bayyana cewa dole sai kungiyoyin addini na kasa sun shiga sahun gaba, saboda yakin na addini ne.

Shugaban rundunar sojin ya ce akwai bukatar kungiyoyin addini su shigo cikin lamarin yaki da ta'addanci saboda 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram da ISWAP na kafa hujja da addini.

Buratai ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wurin wani taron wayar da kai da aka shirya a cibiyar sojoji da ke Abuja domin tattauna wa a kan yadda za a shawo kan aiyukan ta'addanci a Najeriya ta hanyar yakar zazzafar akidar addini.

Shugaba sojojin, wanda manjo janar Sani Yusuf ya wakilta, ya bukaci malaman addinin Islama da na Kirista da ke kasar na a kan su shigo a dama da su wajen yaki da ta'addanci da kuma canja tunanin mutane a kan riko da akidu marasa kyau.

A cewar Buratai, "abu ne mai sauki mu samu galaba a kan 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram da ISWAP, amma ba abu ne mai sauki ba mu samu galaba a kan yakar akidunsu.

DUBA WANNAN: Zunubin ya ishen haka, na shafe shekaru 13 mu na soyayya da mijin 'yar uwa ta - Budurwa

"A saboda haka akwai bukatar kungiyoyi, shugabannin al'umma da iyaye su hada hannu wuri guda wajen yakar akidun da ke cusa kaunar ta'addanci a zukatan jama'a.

"Kungiyoyi, musamman na addini, da ke mu'amala da mutane a karkara, ya kamata su shigo a dama da su wajen yaki da ta'addanci da 'yan ta'adda ta hanyar fadakar da jama'a.

"Za mu yi aikin mu, amma ba dakarun soji ne kadai zasu iya kawo karshen aiyukan ta'addanci da 'yan ta'adda ba a Najeriya, ba iya filin daga kadai yakin ya tsaya ba. Akwai rawar da Malaman addini za su taka wajen yaki da akidar da ke bawa 'yan ta'addar karfin gwuiwa, yaki da irin wadannan akidu ya zama wajibi matukar ana son kawo karshen lamarin gaba daya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel