Gwamnati ta bi umarnin kotu, ta saki Sowore - Nicholas Tofowomo

Gwamnati ta bi umarnin kotu, ta saki Sowore - Nicholas Tofowomo

Sanata Nicholas Tofowomo mai wakiltar yankin Kudancin jihar Ondo, ya yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta bi abin da Alkalai su ka ce, ta bada belin Omoyele Sowore.

‘Dan majalisar na PDP ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi wata hira ta musamman da Jaridar Legit.ng. Sanatan ya shiga cikin sahun sauran ‘Yan Najeriya da ke kira domin a saki Yele Sowore.

Nicholas Tofowomo wanda shi ne ke wakiltar Mazabar Yele Sowore a majalisar dattawa ya bayyana cewa damukaradiyyar Najeriya na ci baya muddin gwamnati ta na sabawa umarnin kotu.

“A lokacin mulkin Soja ne kowane hukunci kotu ta yanke, sojoji na iya warware shi. Muddin kotu ta na cin gashin kanta a tsarin dokar kasa, bai dace gwamnatin tarayya ta yi kokarin taka su ba.” Inji sa.

KU KARANTA: Lauyoyin Najeriya sun yi Allah-wadai da tsare Yele Sowore

Sanata Nicholas Tofowomo yake cewa sabawa hukuncin kotu ya zama wani tambari na mulkin Soji. “Abin da na yi amanna da shi a nan shi ne, kotun shari’a ta ce a saki Omoyele Sowore."

"Idan gwamnatin Najeriya za ta sabawa hukuncin da kotu ta dauka, mulkin farar ya na samun tasgaro a kasa domin a lokacin Soja ne kurum gwamnati ta ke watsawa Alkalai kasa a idanu.”

Wannan ne karon farko da ‘dan majalisar dattawan ya yi kira ga hukuma da gwamnati ta bi abin da Alkalan kotu su ka fada na cewa a saki 'dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar AAC a 2019.

A yau Ranar 30 ga Watan Satumban 2019 ne Yele Sowore ya bayyana a gaban kotu a karon farko cikin koshin lafiya. Sowore ya na tare da Olawale Bakare, wanda ake zarginsa da laifi tare da shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel