An zo wurin: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukuncin a shari'ar zaben gwamnan jihar Sokoto

An zo wurin: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukuncin a shari'ar zaben gwamnan jihar Sokoto

Kotun sauraron korafin zaben gwamnan da ke zamanta a jihar Sokoto ta tsayar da ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci. Kotun za ta yanke hukunci ne a Abuja, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Duk da kotun ba ta bayar da da wani dalili na yanke hukunci a Abuja ba, Daily Trust ta ce kotun ta yi hakan ne saboda dalilan tsaro.

Barista Bashir Jodi, daya daga cikin lauyoyin da ke da hannu a cikin shari'ar, ne ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa kotun za ta yanke hukunci ranar Laraba a Abuja.

Ku san dukkan kotunan sauraron korafin zabe da aka kafa a jihohi da dama sun kammala aikinsu, sun yanke hukunci.

Sokoto, Kano, Bauchi da Filato na daga cikin tsirarun jihohi da har yanzu jama'a ke cigaba da dakon hukuncin da kotu zata zartar a kan karar da ke gabanta.

DUBA WANNAN: Ta leko ta koma: Sanatoci 4 da kotu ta soke zabensu

A jihar Sokoto, dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Alhaji Ahmed Aliyu, ya garzaya gaban kotun sauraron korafin zabe domin kalubalantar nasarar da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewa gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ya samu da banbancin kuri'un da basu kai 500 ba.

A zama na bayan bayan nan da kotun ta yi, hukumar zabe ta kasa (INEC) ta gaza gabatar da shaida ko daya a cikin shaidu 12 da ta yi ikirarain za ta gabatar a gaban kotun, lamarin da ya bawa lauyoyin kowanne bangare mamaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel