Ta leko ta koma: Sanatoci 4 da kotu ta soke zabensu

Ta leko ta koma: Sanatoci 4 da kotu ta soke zabensu

A yayin da 'yan siyasar da aka zaba a kujeru daban-daban suka fara gyara zama domin tunkarar aiyukan da ke gabansu, wasu daga cikinsu sun shiga halin damuwa bayan sun fara ganin alamun 'ta leko, ta koma'.

A kalla sanatoci hudu ne ya zuwa yanzu kotu ta yanke hukuncin soke zabensu a cikin kasa da watanni hudu da rantsar da su a matsayin mambobin majalisar dattijai.

Kotunan sauraron korafin zabe daban-daban sun zartar da hukuncin soke zaben sanatocin tare da bayar da umarnin sake gudanar da sabon zabe a yankunansu.

Sanatocin da ke fuskantar barazanar 'ta leko, ta koma' sune kamar haka:

1. Orji Uzor Kalu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da sunan tsohon gwamnan jihar Abia Mista Orji Uzor Kalu, mamba a jam'iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben takarar kujerar majalisar dattijai ta yankin jihar Abia ta arewa.

A cewar INEC, Kalu ya samu nasarar lashe zaben da adadin kuri'u 31,203, yayin da abokin takararsa, Mista Mao Ohabunwa, dan jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 20,801, kamar yadda baturen zaben yankin, Charles Anumudu, ya sanar a watan Fabarairu.

Dan takarar PDP, Mista Ohabunwa, mai neman tazarce a karo na biyu, ya yi watsi da sakamakon zaben da INEC ta sanar tare da garzaya wa kotu domin nema ta soke zaben Kalu bisa hujjar cewa an tafka magudi kuma duk da hakan banbancin kuri'un da ke tsakaninsu ya gaza adadin kuri'un da suka lalace.

Bayan kotun sauraron korafin zabe ta zartar da hukuncin cewa ta soke zaben tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a wasu mazabu a cikin kwanaki 90, Kalu ya daukaka kara domin kalubalanatar hukuncin kotun.

2. Sanata Dino Melaye

Sanatan jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya sake lashe takarar kujera mamba a majalisar dattijai a karo na biyu, kamar yadda INEC ta sanar da sakamakon zabensa a watan Fabrairu.

Da yake sanar da sakamakon zaben, baturen zabe, Emmanuel Bala, ya ce Melaye ya samu kuri'u 85,395, yayin da abokin karawarsa, Smart Adeyemi, dan jam'iyyar APC, ya samu kuri'u 66,901.

Kotun sauraron korafin zabe karkashin jagorancin, Anthony Chijioke, ta soke zaben Melaye bisa kafa hujja da cewa an tafka magudi, tare da bayyana cewa sakamakon da aka sanar ba shine abinda jama'a suka zaba ba.

Tuni Melaye ya garzaya gaban kotun daukaka kara da ke Abuja domin kalubalantar hukuncin kotun.

3. Adedayo Adeyeye

Sanata mai wakiltar jihar Ekiti ta kudu, Adedayo Adeyeye, ya zama kakakin majalisar dattijai bayan an bayyana sunansa a matsayin shugaban kwamitin sadarwa da hulda da jama'a na majalisar dattijai.

A cewar baturen zabe, Laide Lawal, Adeyeye ya samu nasarar lashe zabe a karkashin inuwar jam'iyyar APC da jimillar kuri'u 77,621, yayin da abokiyar karawarsa a jam'iyyar PDP, Biodun Olujimi, tsohuwar shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai, ya samu kuri'u 53,741.

Uwargida Olujimi ta garzaya gaban sauraron korafin zabe tare da neman a bayyana ta a matsayin wacce ta samu nasara a zaben saboda ita ce ta samu mafi rinjayen kuri'u na halali a zaben.

A cikin watan Agusta ne kotun ta yanke hukuncin soke zaben Adeyeye tare da bayar da umarnin rantsar da Olujimi a matsayin wacce ta lashe zaben.

Adeyeye ya yi watsi da hukuncin kotun tare da garzaya wa kotun daukaka kara domin kalubalanatar hukuncin kotun.

4. James Manager

Hukumar INEC ta bayyana sunan James Manager, dan jam'iyyar PDP, a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben kujerar sanatan jihar Delta ta kudu.

Oladipupo Adesina, baturen zabe, ya ce Manager ya samu kuri'u 2528,812, yayin da abokin takararsa, tsohin gwamnan jihar Delta, Emmanuel Uduaghan, dan jam'iyyar APC, ya samu kuri'u 125,776.

Uduaghan ya nufi kotun sauraron korafin zabe tare da bukatar neman ta soke zaben Manager bisa zargin cewa an tafka magudi.

A hukuncin da ta yanke, kotun ta soke zaben Manager tare da umartar hukumar INEC ta kwace takardar shaidar cin zabensa tare da bayar da umarni sake zabe a cikin kwanaki 90.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel