Monday Obolo ya zama kakakin majalisar dokokin Bayelsa bayan yan bindiga sun kwace sandar iko

Monday Obolo ya zama kakakin majalisar dokokin Bayelsa bayan yan bindiga sun kwace sandar iko

Wani mamba mai wakiltan mazabar Kudacin Ijaw II, Monday Obolo, ya zama sabon kakakin majalisar dokokin jihar Bayelsa.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan an jiyo karar harbe-harbe a harabar majalisar dokokin jihar jim kadan bayan tsojon kakakin majalisar ya tsere da sandar iko.

Rahotanni sun kawo cewa mamayar na da nasaba da rikicin shugabanci na bangaren zatarwa kan matsin lamba da ta sanya wa kakaki majalisar Tonye Isenah da kan yayi murabus domin bayar da hanyar da Shugaban masu rinjaye a majalisar, Monday Obolo domin ya zama sabon kakakin majalisar.

A ranar Juma’a ne Mista Isenah ya bayyana wa abokan aikinsa da ma’aikatan majalisar dokokin cewa zai yi muabus a yau amma a lokacin da yan majalisar ke ganawar sirri, sai yan bindiga suka kai mamaya zauen majalisar sannan suka tsere da sadar iko.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Zamfara ta sa ayi bincike akan batun sanya Qur’ani a najasa, tayi alkawarin bayar da naira miliyan 2 ga duk wanda ya kawo bayanai

Mista Monday Obolo na kudancin Ijaw II ya zama sabon kakakin majalisa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kula sun tashi a zauren majalisar dokokin jihar Bayelsa da safiyar yau Litinin yayinda aka fara jin harbe-harbe bindigogi yayinda kakakin majalisar ya gudu da sandar majalisa.

Wannan ya biyo bayan rikice-rikicen siyasan da ke gudana cikin gidan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar da zai gudana a watan Nuwamba, 2019.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel