Rundunar sojin Najeriya ta kama mutumin da aka zarga da kai wa Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojin Najeriya ta kama mutumin da aka zarga da kai wa Boko Haram kayayyaki

Rundunan Sojin Najeriya a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumba, ta kama wani mai kai wa yan ta’addan Boko Haram kayyayaki sannan kuma suka kwace mota dauke da tayoyin mashina a Borno.

A.K Ibrahim, Mukaddashin Babban kwamandan (GOC) 7 Division ne ya bayyana haka yayin da ya gurfanar da mai laifin a babbar sansanin Gubio dake Maiduguri.

Mista Ibrahim ya bayyana cewa tawagar rundunan Operation Lafiya Dole da kuma Jami’an hukumar kwastam ne suka kama mai laifin, Samuel Chukwudon a ranar 27 ga watan Satumba yayin da yake tafiya a hanyar Baga-Monguno.

Ya bayyana cewa rundunar ta kama kayayyakin da suka hada da mota, tayoyi 136 na mashina, sabbin tube guda 200 da kuma gam.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Zamfara ta sa ayi bincike akan batun sanya Qur’ani a najasa, tayi alkawarin bayar da naira miliyan 2 ga duk wanda ya kawo bayanai

Jami’in ya bayyana cewa za a lalata mota da kuma kayan da aka kama, ya kuma gargadi mutane masu cinikin babura da kayayyakin bubaran.

Sai dai mai laifin ya bayyana ma manema labarai cewa yana siyar da tayoyin ga masu siyar da ruwa da masu siyar da itatuwa a Monguno.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel