Yanzu-Yanzu: Harbe-harbe, rikici ya barke a majalisar dokokin Bayelsa yayinda Kakaki ya sace sandar majalisa

Yanzu-Yanzu: Harbe-harbe, rikici ya barke a majalisar dokokin Bayelsa yayinda Kakaki ya sace sandar majalisa

Hankula sun tashi a zauren majalisar dokokin jihar Bayelsa da safiyar yau Litinin yayinda aka fara jin harbe-harbe bindigogi yayinda kakakin majalisar ya gudu da sandar majalisa.

Wannan ya biyo bayan rikice-rikicen siyasan da ke gudana cikin gidan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar da zai gudana a watan Nuwamba, 2019.

An bukaci kakaki majalisar dokokin jihar, Tonye Isenah, yayi murabus domin kwantar da kuran siyasar.

Jigogin jam'iyyar PDP sun kunna masa wuta kuma rahotannin da aka samu a ranar Juma'a, 27 ga Satumba sun nuna cewa kakakin ya amince daga karshe yayi murabus da safen nan idan majalisa ta dawo zama.

Amma yayinda aka hallara a zauren majalisa yau, kakaki Isenah, ya sace sandar majalisar kuma ya gudu da ita.

Kalli bidiyo:

Ku saurari cikakken rahoton..

Asali: Legit.ng

Online view pixel