Nigeria@59: Najeriya ba lafiya - Atiku Abubakar ya yi korafi

Nigeria@59: Najeriya ba lafiya - Atiku Abubakar ya yi korafi

- Atiku Abubakar yace babu lafiya a Najeriya a yanzu tunda kasar ta zamo hedkwatar tsantsar talauci a duniya

- A sakonsa zuwa ga yan Najeriya a bikin zagayowar ranar yancin kai, ya kara da cewa bata karewa Najeriya ba, yace akwai babban rabo anan gaba

- Dan takarar Shugaban kasar na PDP ya bukaci yan Najeriya da suyi aiki domin inganta kasar

Dan takararta Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a sakonsa na cikar kasar shekara 59 da samun yancin kai, yayi korafi akan halin da kasar ke ciki.

A cewarsa, magabatan kasar ba za su taba tunanin cewa bayan shekara 59 da samun yancin kai, Najeriya zata tsinci kanta a hali na rashin yanci ga Jarida da matasa ba, sannan kuma masu rajjin kare hakkin dan Adam ma na fuskantar barazanar kamu.

Da yake cigaba da bayani, Atiku ya bukaci yan Najeriya da su dauki matakin damokradiyya domin tabbatar da cewa ba a yi watsi da kudirin magabatanmu na kawo hadin kai, zaman lafiya da cigaba ba.

KU KARANTA KUMA: Katsina: An siyar da mutane 20 da aka yi garkuwa da su a matsayin bayi a Burkina Faso

Atiku ya kuma bukaci al'umman kasar da suyi aiki tare da jajircewa domin inganta kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel