Boko Haram: Magu ya nemi a rika lura da masu yawo da tsabar kudi

Boko Haram: Magu ya nemi a rika lura da masu yawo da tsabar kudi

Shugaban rikon kwarya na hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, Ibrahim Magu, ya yi kira ga Sojoji su takaita yawo da kudi da ake yi a yankin Boko Haram.

Ibrahim Magu ya nemi shugaban Dakarun sojojin Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ya tabbatar ana duba kungiyoyi masu zaman kansu wajen zirga-zirga da tsabar kudi.

Magu yake cewa ya kamata a rika sa ido har ta kai sai hukuma ta bada dama kafin wata kungiya ta rika kai-komo da dukiya a yankin Arewa maso Gabas inda ake fama da rikicin Boko Haram.

Mukaddashin shugaban na EFCC ya na ganin cewa wannan kaidi da za a yi wa kungiyoyin da ke aiki a Arewa ta Gabas zai taimaka wajen dakile ta’adin da ‘yan ta’adda su ke yi da makudan kudi.

KU KARANTA: Hukumar EFCC da Malami za su bayyana adadin dukiyar Maina da aka rike

Mista Magu yake cewa EFCC ta dade ta na sa ido a kan wadanda ke aiki a matsayin masu bada taimako da agajin gaggawa a bangaren kasar inda har gobe ake yakar ‘yan ta’addan Boko Haram.

Shugaban rikon kwaryar ya yi wannan jawabi ne ta bakin shugaban EFCC na shiyyar Maiduguri watau Lawrence Iwodi, a lokacin da ya kai ziyara zuwa barikin Sojin nan na Maimalari da ke jihar.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, shi ne ya fitar da jawabi kan yadda ganawar hukumar da jami’an tsaron ta kasance. A na su bangaren, Sojin sun yabawa irin kokarin da EFCC ta ke yi a yankin.

EFCC ta tara sunayen duk kungiyoyin da ke aiki a Borno da Yobe kuma ana lura da masu yawo da kudin da ya haura miliyan guda domin ganin bayan Miyagun da ke fakewa da sunan kungiyoyin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel