Yaki da Iran zai durkusar da tattalin arzikin duniya - Yarima MBS

Yaki da Iran zai durkusar da tattalin arzikin duniya - Yarima MBS

Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado, Muhammad bin Salman, a hirar da ya gabatar ranar Lahadi ya bayyana cewa fito na fito da kasar Iran zai illanta tattalin arzikin duniya.

Ya bayyana cewa ya gwammace a yi zaman sulhu da siyasa maimakon yaki.

Yarima Mohammed bin Salman ya kara da cewa idan aka shiga yaki a yanzu, farashin danyen mai zai iya tashin da ba'a taba tunani ba.

Yace: "Wannan yankin na da arzikin man kashi 30 cikin 100 na duniya, kashi 20 cikin 100 na hanyoyin kasuwanci, kimanin kashi 4 na tattalin arzikin duniya."

"Yanzu me kake tunani idan dukkan wannan ya tsaya. Hakan na nufin durkushewar tattalin arzikin duniya, ba Saudiyya ko kasashen larabawa kadai ba."

Ya yi kira ga shugabannin duniya da a dauki matakin dakile Iran da kuma samar da zaman lafiya.

KU KARANTA: Ku nada kashi a gindi - Cewar kotu akan Shekarau, Wali, da Ahmed

Yariman ya amince da jawabin sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, cewa harin da aka kai kamfanin man feturin Saudiyya, Aramco, aikin kasar Iran ce.

A ranar 14 ga Satumba, an kai harin bam kamfanin man feturin Saudi Aramco kuma kasar Amurka da wasu kasashen Turai sun yi ittifakin cewa da hannun Iran a ciki.

Kasar Iran ta karyata wannan zargi kuma ta bukaci masu zarginta da suka kawo hujjan ikirarinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel