Katsina: An siyar da mutane 20 da aka yi garkuwa da su a matsayin bayi a Burkina Faso

Katsina: An siyar da mutane 20 da aka yi garkuwa da su a matsayin bayi a Burkina Faso

Rahotanni sun kawo cewa an siyar da akalla mutane 20 da aka yi garkuwa dasu a jihar Katsina a matsayin bayi a Burkina faso.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an yi garkuwa da mutanen ne a karamar hukumar Kankara da ke jihar sannan aka siyar dasu zuwa ga wata mata a Kwatano wacce ita kuma ta siyar dasu ga wani mai cinikin ayi a Burkina Faso.

Ku tuna cewa gwamnatin jihar Katsina da Gwamna Aminu Bello Masari sun kaa shirin sasanci inda suka ziyarci mafakar yan bindiga domin kulla yarjejeniya tare da shirin chanjiya inda suka saki mutanen da aka yi garkuwa da su sannan su kuma suka saki yan bindigan.

Wata majiya ta bayyana cewa babu mamaki Gwamnan ya bibiyi inda aka kai mutanen a Burkina Faso sannan cewa ya shirya tsarin ceto mutanen 20 na jiharsa da aka siyar a matsayin bayi.

Majiyar tace hadimin gwamnan na musamman kan kwayoyi da safarar mutane, Alhaji Brodo ya tafi Burkina Faso domin tattauna batun sakinsu.

KU KARANTA KUMA: Wasu yan fashi 3 sun hadu da ajalinsu a hannun fusatattun matasa a jihar Benue

Da yake tabbatar da lamarin, Brodo yace: “Kwarai zai tafi Burkina Faso a karshen makon nan.

“Zan dai san idan wadannan mutane 20 yan asalin Katsina ne bayan na hadu dasu da wadanda suka yi garkuwa dasu,” inji Brodo.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel