Dalilin mu na kai wa Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ziyara – Inji Kungiyar CAN

Dalilin mu na kai wa Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ziyara – Inji Kungiyar CAN

Kungiyar Kiristocin Najeriya na CAN sun bayyana abin da ya sa su ka kai wa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ziyara. An rahoto wannan ne a Ranar 30 ga Satumban 2019.

CAN ta ce ta taka kafa ya kafa zuwa ofishin mataimakin shugaban na Najeriya ne domin jin bangaren na sa labarin game da zargin da ake yi masa na cewa ya karbi wasu makudan Biliyoyi.

Shugaban wannan kungiya ta Mabiya addinin Kirista, Rabaren Samson Ayokunle, ya bayyana wannan ta bakin wani Hadiminsa na yada labarai mai suna Bayo Oladeji a karshen makon jiya.

Samson Ayokunle yake cewa ziyarar da su ka kai wa Osinbajo ba ta sabawa doka ba, sannan kuma ya ce wannan ba ya nufin su na yi wa mataimakin shugaban Najeriyar wata mubaya’a.

Rabaren Ayokunle ya kara da cewa ba za su taba marawa maras gaskiya baya ba, sannan kuma yace kungiyar ba ta taba dauke zargi daga kan wanda ake zargi ba domin kuwa ita ba kotu bace.

KU KARANTA: Malami Bakare ya leka ya gano karshen Yemi Osinbajo

“Duk wanda ake zargi da rashin gaskiya zai kare kansa da hujjoji a kotun shari’a kafin a wanke sa kamar yadda mu ka sani. Mu ba kotu ba ne da ke yanke hukuncin shari’a” Inji Ayokunle.

CAN ta ce: “Bayan mun zauna da shi (Osinbajo), ya fada mana cewa zargin bai da tushe kuma soki-burustu ne, bayan haka kuma zai tafi kotu ayi shari’a domin ya kare kansa gaban kuliya.”

Mun tabbatar masa da cewa idan har aka gano tabbas bai da laifi, a lokacin za mu taru mu mara masa baya. Bayan nan mun yi masa addu’a, sannan mu ka yi wa kasar mu Najeriya addu’o’i.”

A karshen jawabin na CAN, kungiyar ta ce tun ba yau ba, ta yabawa kokarin da gwamnatin Buhari ta ke yi na yaki da cin hanci da rashawa, sai dai ta kara kira a daina nuna banbanci wajen yakin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel